19 Afirilu 2022 - 19:59
Kasar Afirka Ta Kudus Ta Sanar Da Kafa Dokar Ta Baci Dangane Da Bala’in Dabi’a

Shugaban kasar ta Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da kafa dokar a kasar, mako daya bayan da wani ambaliyar ruwa da aka yi, wanda ya ci rayukan mutane 443 a Durban dake gabar ruwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A jawabin da ya yi ta kafar wata labrun kasar a jiya Litinin, shugaba Ramaphosa ya ce; A wannan lokacin, dukkaninmu muna cikin halin alhini, tare da bayyana abinda ya faru da cewa;Bala’i ne”

Tuni dai gwamnatin kasar ta aike da sojoji 10,000 zuwa yankunan da bala’in ya shafa domin gudanar da ayyukan agaji da ceto.

Yankin Kwazulu-Natal da ya fuskanci ambaliyar ruwa da kuma zaizayar kasa ne aka fi samun wadanda lamarin ya rutsa da su.

Cibiyar da take kula da yanayin sararin samaniyar ta kasar Afirka Ta Kudun, ta ce a halin yanzu an sami saukin saukar ruwa sama, amma ana hasashen cewa a kwanaki masu zuwa za a iya fuskantar wata ambaliyar ruwa.

Dubban mutane dai su ka rasa muhallansu, a wasu yankunan kuma babu ruwan sha ko wutar lantarki.

342/